Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Binciken bayanai ya nuna cewa tun farkon aiwatar da shingen da Amurka ta sanya kan jiragen ruwa masu alaƙa da tashoshin Iran a ranar 13 ga watan Afrilu da ya gabata, har zuwa ranar 30 ga Afrilu, jiragen ruwa 81 ne suka ketare mashigar Hormuz suna saba wa dokar Amurka, daga cikin jirage 145 da suka wuce a wannan lokacin. Wannan ya kai kusan kashi 56% na zirga-zirgar da aka yi tun bayan fara aiki da dokar Amurka.
Wani bincike na bayanai daga dandalin Marine Traffic, an gano cewa jiragen ruwa 53 ne suka ketare mashigar Hormuz suna masu karya dokar Amurka, wadannan jiragen ko dai sun taso daga tashoshin jiragen ruwa na Iran ko kuma suna tafiya zuwa garesu, ko kuma suna ɗauke da tutar Iran, ciki har da jiragen ruwa 11 da suke cikin jerin takunkumin Amurka.
Haka kuma, wasu jiragen ruwa 28 sun ketare mashigar suna cikin jerin takunkumin Amurka, amma ba su da alaƙa da tashoshin Iran. Don haka jimillar jiragen ruwa da suka saba wa dokar Amurka tun farkon aiwatar da shingen ya kai 78.
Binciken ya dogara ne akan lura da kwatankwacin wucewar jiragen ruwa waɗanda suka kunna na'urar bin diddigin su a lokacin da suke ketare mashigar Hormuz.
Binciken ya kuma nuna cewa wasu jiragen ruwa suna kashe na'urar siginar su kafin wucewa, wanda ke nufin alkaluman da ke cikin binciken na iya ƙaruwa sosai.
Tun da farko, rundunar kwamandan Amurka (CENTCOM) ta bayyana cewa shingen yana dai-dai da jiragen ruwa masu shiga ko fita daga tashoshin jiragen ruwa na Iran, ba tare da ya shafi jiragen da ke wucewa tsakanin tashoshin da ba na Iran ba ta mashigar Hormuz.
Amurka ta tara akalla jiragen ruwa 15, ciki har da wani jirgin dakon jiragen sama (aircraft carrier) da kuma masu kai harin tarwatsawa (destroyers) 11, a yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda gidan talabijin na CNN ya ruwaito daga wani jami'in Amurka.
Amma bayanan bin diddigin a cikin sa'o'i 24 na farko na aiwatar da dokar sun nuna cewa Iran ba ta kula da dokar Amurka ba, inda jiragen ruwa 5 masu ɗauke da tutar Iran suka ketare mashigar Hormuz, yayin da wasu jiragen ruwa 6 ke da alaƙa da tashoshin Iran, ko suna fita daga garesu ko kuma suna tafiya zuwa garesu.
Yayin da rundunar CENTCOM ta bayyana cewa ta karkatar da hanyoyin jiragen ruwa 39 da suka saba wa dokar, bayanan bin diddigi sun nuna cewa jiragen ruwa 50 sun fice daga mashigar Hormuz suna tafiya daga ko zuwa tashoshin Iran.
Binciken ya kuma nuna cewa jiragen ruwa da suka saba wa dokar Amurka sun bambanta da nauyin kayayyakin da suke ɗauke da su, inda suka haɗa da jiragen dakon kaya da kwantena 36, jiragen dakon kaya masu yawa (bulk carriers) 11, da kuma jiragen dakon mai 6.
Ranar 28 ga watan Afrilu da ke wannan shekara ita ce ranar da aka sami mafi yawan wucewar jiragen ruwa da suka saba wa dokar Amurka, inda jiragen ruwa 10 suka ketare mashigar a bangarorin biyu. Wannan a fili yake nuna cewa wucewar jiragen ruwan Iran ta mashigar yana ƙaruwa yayin da barazanar Amurka ke taɓuwa.
Tun da farko, sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kama wani jirgin dakon mai mai suna TIFANI a cikin tekun Indiya, da zargin cewa yana ɗauke da ganga miliyan biyu na man fetur da aka loda daga tsibirin Kharak na Iran.
Har ila yau, sojojin sun kame wani jirgin dakon kwantena mai suna TOUSKA wanda ke ɗauke da tutar Iran a cikin tekun Oman, kimanin kilomita 47 daga gaɓar tekun Iran.
A nasa bangaren, shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce duk wani yunƙuri na sanya shingen ruwa ko kuma takunkumi da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, ba zai yi nasara ba.
Your Comment